![]() |
| MACE |
A farkon wannan watan ne kasar Sifaniya ta soma shirin samar da wata doka da za ta bayar da hutu ga mata ma'aikata da ke faɗawa mawuyacin hali lokacin da suke jinin al'ada.
Daftarin dokar ya bayyana cewa za a iya bai wa mace hutun kwana uku a duk wata - kuma ana iya tsawaitawa zuwa kwana biyar a wasu lokuta.
Mene ne jinin al'ada?
Jinin al'ada shi ne fitowar jini daga mahaifar mace, hakan na faruwa ne sakamakon wasu sauye-sauye da mata kan fuskanta a kowanne wata ko kwanakin da ba su kai wata guda ba.
Dakta Zainab Dan-Yaya, likita a Federal Medical Centre a Jabi da ke Abuja babban birnin Najeriya, ta ce jinin na fitowa ne a lokacin da mace ta saki kwan haihuwa, wani yakan zama da idan lokacin daukar ciki ya yi ba kuma tare da mace tana amfani da wani nau'i na kayyade iyali ba.
Wasu matan kan fara ganin jinin al'ada daga shekaru 12 har zuwa 15, ya danganta da yanayin mace.
Sai dai Dr Zainab ta ce saboda sauyawar yanayi da zamani akan samu yara matan da kan fara jinin al'adar suna da shekara tara.
Ma'ana wasu kan fara da kankantar shekaru sai kuma ya dauke ba zai sake dawowa ba sai kuma bayan wasu shekaru, wasu da zarar sun fara shi ke nan zai ci gaba a haka har zuwa shekarun girma da yake daukewa baki daya tamkar mace ba ta taba yi ba.
Yawan kwanakin jinin al'ada ya kasu kashi daban-daban, wasu kan yi kwana huɗu, wasu mako guda, wasu kan yi har makonni biyu.
To amma da zarar wannan lokaci ya haura, ana bai wa mata shawarar zuwa asibiti domin ganin likita da tabbatar da cewa ba wata matsala ko lalura ce ta samu mace ba.
Wasu matan kan fuskanci matsananciyar rashin lafiya, a lokacin da za su fara jinin a karon farko, wasu kuma kan fuskanci matsanancin ciwo a kowanne wata, ko dai kwanaki biyu gabannin zubar jinin ko kuma idan su na tsaka da yi.
Kadan daga cikin matsalolin da wasu matan, kan fuskanta a lokacin da suke jinin al'ada:
- Wasu matan kan fuskanci matsancin ciwon baya, da ya kan janyo musu kasa zama sai kwanciya
- Sukan fuskanci ciwon gaɓɓai, hakan na saukar da kasala da rashin kuzari
- Matsanancin ciwon kai, da zazzabi, wasu matan kan haɗa da amai
- Wasu ma kan yi amai da gudawa, ko kuma gudawar gabanni da lokacin jinin al'ada ko kuma bayan sun kammala
- Wasu kuma lamarin kan zo musu da yawan bacci, duk inda suka samu sai kwanciya
- Akwai kuma matsancin ciwon mara da ta ke daurewa da hakan kan sanya mace durkushewa da matsa ciki da mara. Ba raggwantaka ba ce idan mace ta yi kuka a wannan yanayin tsananin ciwon kan haddasa takura
- Sannan wasu kuma za su dinga shiga yanayi na ƙunci da ɓacin rai ne ba gaira ba dalili, ko jin haushin na kusa da su
- Wasu kuma tashin zuciya da ɗan kwaɗayi-kwaɗayi suke fama da shi kamar irin na masu ciki.
Wasu matan kan fara ciwon kafin lokacin al'adar, da kuma lokacin da suke yi, wasu kuma sai sun kammala.
Akwai wasu nau'in matan da suke yin ciwon tun kafin su fara da tsakiyarsa har zuwa karshe.
Dakta Zainab ta ce wasu matan na danganta ciwon mara lokacin jinin al'ada da kuma ciwon nakuda, sakamakon yadda ko ina a jikinsu ke amsawa tun daga kugu da baya, da mara da kafa da dukkan gabban jiki.


